Skip to main content
*DARULHIKMA HERBAL MEDICINE*
☎08032652765 ko 08059686500
WhatsApp 08026981388

 *AKWAI WANI ABU MUHIMMI DA MATA YAKAMATA SU SANI DANFANE DA AL'AURARSU(farji*)

Akwai wasu bayanan da ba na gaskiya ba da ke kai komo a shafukan sada zumunta dangane da al'aurar mata, kuma wata mace ta dauki gabarar gyara irin wannan tunanin.
08032652765

Dr Jen Gunter, wadda likitar mata ce ta kwashe shekaru 25 tana aikin kula da lafiyar mata a Amurka da Canada. Har wa yau, ana bayyana Dr Jane mai fafutukar lafiyar mata a shafukan Twitter.

A baya-bayan ta tunkari wani camfi da ke cewa cusa kwai mai tauri a cikin al'aurar mace na taimakawa wajen samun daidaito a lokacin al'ada da kuma sarrafa mafitsara.

Dr Jane ta nuna cewa ikrarin sam ba ya cikin tsofaffin al'adun mutanen kasar Sin kuma ba su da madogara a kimiyyance. Hakan ya sa aka yi watsi da camfin.
08032652765

Littafin Dr Gunter da ta wallafa a baya-bayan nan shi ne 'The Vagina Bible' wato 'Kundi kan abin da ya shafi al'aurar mata,' ya kasance littafin da aka fi rububin nema a kasashe da dama.

Littafin na kunshe da shawarwari na hakika domin kara wa matan sani kan yadda za su inganta rayuwarsu. Dr Jane ta zayyana wasu abubuwa da take ganin ya kamata duk wata mace ta sani.
08032652765

Hakkin mallakar hotoEMMA RUSSELL
 *1 - Muhimmancin sanin al'aura tun daga dumbaru*

Ita al'aurar mace na cikin jikinta ne, wato wata kafa ce da ta hada mahaifar mace da wajen al'aurarta. Fatun da ke taba fatarin mace su ne ake kira da dumbaru.

Gunter na da fahimtar cewa sanin bambanci tsakanin abubuwan guda ka iya taimaka wa mata wajen sanin hakikanin abin da ke damun su idan suka samu larurar da ta shafi matantaka.
08032652765

 *2 Al'aura na tsaftace kanta*

Gunter ta fajimci cewa an samu sauyi a shekara 10 da suka gabata, inda da dama daga cikin mata ke amfani da wasu abubuwa domin kyautata kamshin gabansu.

Kusan kaso 57 da matan Arewacin Amurka ne suke wanke gabansu a 'yan shekarun da suka gabata, inda wasu ke fadin mazajensu ne ke ba su shawarar yin hakan.

To sai dai Gunter ta ce babu bukatar yin amfani da wani abu domin wanko cikin al'aurar mata.

"Wani bututu ne da ke wanko kansa," in ji Gunter.

Gunter ta kuma yi gargadi kan amfani da abubuwa masu kamshi.

"Ita al'aurar mace ba ta son bakon abu."

Ko da ruwa ka iya kawo cikas ga tsarin halittar gaban mace, ta hanyar janyo kamuwa da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i. Shi ma turaren da ake yi wa al'aura ka iya janyo konewarsa.

Ana iya amfani da ruwa wajen tsaftace dumbaru idan har ya zama dole.

Yin amfani da sabulu ka iya debe yadin fata wanda ke yi wa fatar dan adam garkuwa. Idan mace ta kai shekarun daukewar jinin al'ada, za ta iya amfani da man kwakwa ko kuma na zaitun.

Ana samun sauyin kwayoyin halittar farjin mace a duk sa'a 96, fiye da sauyin da fata take samu a sauran sassan, saboda haka za su fi saurin samun waraka.

Hakkin mallakar hotoEMMA RUSSELL
 *3 - Al'aura tamkar lambu ne*
08032652765

Gaban mace na kunshe da kwayoyin bacteria 'masu kyau' da ke bayar da kariya ga al'aurar.

"Al'aurar mace kamar lambu ne mai dauke da kwayoyin bacteria iri-iri da ke aiki tare don tabbatar da cewa al'aurar na da koshin lafiya," in ji Gunter.

Kwayoyin bacteria 'masu kyau' na samar da yanayi mai dan zafi, wanda ke hana kwayoyin bacteria 'marasa kyau' samun wurin zama, da kuma majina da ke tabbatar da cewa al'aurar ta kasance a jike ko yaushe.

Shi ya sa goge cikin al'aura da jikakken tsumma ba shi da amfani- yana da amfani ta kasance da kwayoyin bacteria 'masu kyau'.

Haka kuma, Gunter ta bayar da shawarar cewa a daina amfani da injin busar da gashi wajen busar da al'aura: ana bukatar fatar al'aura ta kasance a jike.

Hakkin mallakar hotoEMMA RUSSELL

 *4 Akwai dalilin da ya sa aka halicci gashi a jikin
al'aura 08032652765

Gunter ta lura cewa akwai karuwar mata masu aske gashin jikin al'aurarsu. Wannan na taimakawa wajen hana kwarkwata yaduwa a wajen, amma akwai hadari a tattare da hakan.

"Idan aka aske ko aka cire gashin, kina jin ciwo a fata," in ji Gunter. "Muna ganin yanka ko kujewa har ma ya zama gyambo idan aka cire gashin al'aura."

Gunter ta ce idan za a yi aski, a yi amfani da reza mai tsafta sannan a gyara fatar wajen yadda ya kamata.

Kuma Gunter na son mutane su san matakan da suke dauka.

"Gashin da ke jikin al'aura na da amfaninsa, babu mamaki wata garkuwa ce kuma kariya ga fatar wurin," in ji ta.

"Haka kuma, akwai yiwuwar cewa yana taka rawa wajen saduwa saboda ko wane silin gashi daya na hade ne da wata jijiya- shi ya sa idan ana tsige shi yake zafi."

5- Tsufa na shafar al'aura
Bayan tsawon shekaru ana jinin al'ada da

 haihuwa, mace na kai wa shekarun daukewar al'ada. Yawan sinadaran da ke sa mace daukar ciki na yin kasa sosai- kuma raguwar sinadarin oestrogen na shafar al'aura da dumbaru.

Wadannan abubuwan, wanda a da majina ke sawa su zama a jike na iya kankancewa, ko kuma su jawo bushewar al'ada. Wannan na iya sa wa mace ta rika jin zafi lokacin saduwa.

Wannan na iya jefa mace cikin tsananin damuwa, amma Gunter ta ce mafi yawan mata na iya neman taimako daga wajen likita. Kuma wasu na iya sayen mayukan da ake shafawa a al'aura domin ta jike.

"Ina ganin yana da matukar muhimmanci idan mata suka san haka," in ji ta. "Ba sai kin wahala ba." daga shafin BBC hausa.

 *DARULHIKMA HERBAL MEDICINE* Mun kware wajen bincike da gano matsalolin ku domin taimakawa akan cututtuka masu wahalar magani da.  Kamar su shafar Aljanu sihiri da sauransu.  Don karin bayani sai atuntubi cibiyar ra 08032652765 ko 08059686500
 Ko ta adreshin mu na yanar gizo wato
www.darulhikmang.blogspot.com
 Ko email:darulhikmaherbalmedicine@gmail.com
Ko a whatsApp 08026981388

Comments

Popular posts from this blog

AMFANI ZOGALE GUDA GOMA SHA TAKWAS(18 USER's of moringa)

*DARULHIKMA HERBAL MEDICINE* ☎08032652765 whatssApp 08026981388  AMFANIN ZOGALE GUDA GOMA SHA TAKWAS (18) GA JIKIN DAN-ADAM ========================== 08032652765 . 1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer). . 2- Ana shafa d'anyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai. . 3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya. . 4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa. . 5- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa. . 6- Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari. . 7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa 'yar kadan domin maganin ciwon shawara. . 8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne. . 9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono. . 10-Wa...

FA'IDOJI DAGA DARULHIKMA ISLAMIC AND TRADITIONAL MEDICINE

بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على سيدنا محمد وعلى آله وصحبه وسلم؛ FA'IDOJI MUHIMMAI  *DARULHIKMA ISLAMIC AND TRADITIONAL MEDICINE*  ☎08032652765 08059686500 whatsApp 08026981388 * 1>MAGANIN FITSARIN KWANCE. Ana rubuta ayatul kursiyyu آية الكرسي ƙafa tara amma wake-wake akeyi wato uku da `ya`ya da wasali. uku da `ya`ya amma babu wasali. uku babu `ya`ya babu wasali. in angama sai a wanke sai asa ƙasar gidan cinnaka aciki sai asha ashafe mara za ayi haka har kwana uku. IN ALLAH YA YARDA YARO KO YARINYA MASU FITSARIN KWANCE ZASU DAINA KODA SUN MANYANTA NE KO MATAR AURE CE HAKA KO MAGIDANCI NE KUMA KODA FITSARIN NA ISKA NE/ALJANU ZASU DAINA DA IZININ ALLAH. 2>MAGANIN CIWON HAƘORI. Ana rubuta Fatiha ƙafa 19 amma ko wacce da BISMILLAH sai a wanke sai asami BAGARUWA. da TSAMIYA. da SANYA UWAR MAGUNGUNA. da ALIM. sai a dafa su da ruwan rubutun sai a riƙa kuskure baki da shi amma da ɗumi kafin ya huce gaba ɗaya. IN ALLAH YA YARDA DUK TSANANIN CIWON HAƘORI ZA'A SAMI SAUƘI...